Clinton ta gargadi shugabannin Afirka

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton, ta yi kira ga shugabannin Afirka da su aiwatar da sauye sauyen demokradiyya.

Idan ba haka ba kwa, ta yi gargadin cewa, zasu iya fuskantar irin zanga zangar da jama'a ke yi a kasashen Larabawa.

A cikin jawabin farko da wani sakataren harkokin wajen Amirka ya taba yi a taron kungiyar Tarayyar Afirka, Hillary Clinton ta karfafawa kasashen Afirkar gwiwar su daina goyon bayan Kanar Gaddafi na Libiya, duk da irin taimakon kudaden da yake ba kungiyar.

Ta ce ya kamata su nemi kulla dangantaka da 'yan tawayen Libiyar.