Yau ake bikin ba da gudunmawar jini ta duniya

Dakin gwajin jin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yau ake bikin ranar ba da gudunmawar jini

A Najeriya, a yau Talata ne 'yan kasar ke bin sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen bikin ranar ba da gudunmuwar jini.

Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware ranar sha hudu ga watan Yunin kowacce shekara, don karfafa gwiwar mutane wajen ba da gudunmuwar jini ga mutanen da basu da lafiya.

Taken bikin na bana dai shi ne:'Kara bayar da gudunmawar jini, don kara ceto rayuka'.

Sai dai a yayin da wasu 'yan Najeriya ke cewa suna bayar da gudunmawar jinin don radin kansu, wasu sun ce basu taba bayar da gudunmawar jinin ba.

Likitoci a kasar dai, na karfafa gwiwar jama'a da su bayar da gudunwar jinin, inda suka ce hakan bashi da wata illa.