Sudan: Farmakin Kordofan na haddasa wahalhalu

Mazauna Kordofan a Hedikwatar Majalisar dinkin duniya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mazauna Kordofan a Hedikwatar Majalisar dinkin duniya

Majalisar dinkin duniya ta ce dubunnan mutane a Sudan sun rasa matsugunansu sakamakon ruwan bama-bamai da kuma fada akan iyaka da kudancin Kordofan.

Dakarun Sudan sun kaddamar da sabbabin hare-hare kan kan jama'ar dake da alaka da kudancin kasar wacce zata sami 'yancin kai a wata mai zuwa.

Fatima Lejeune-Kaba kakakin majalisar dinkin duniya ce a Afrika, ta ce," akwai akalla mutane dubu arba'in da daya da suka rasa matsugunansu, a ciki da kewayen Kadugli dake kudancin Kordofan, kuma wadannan sune wadanda muka san inda suke."

Majalisar dinkin duniya tace akalla mutane dubu arba'in da daya sun guje, kuma an yi amanna akwai da dama da ba iya kaiwa gare su ba.