'Yan tawaye sun samu sabuwar galaba a Libya

Rahotanni daga Libya sun ce 'yan tawaye sun kara samun nasara kan dakarun gwamnati kusa da garin Misrata dake hannun 'yan tawayen.

Rahotanni suka ce sun kara matsawa daga Misrata zuwa wajen garin Ziltan dake hannun gwamnati.

Wakilin BBC yace,'yan tawayen sun dan kara matsawa, kimanin kilimota guda da rabi.

Lokacin da suke kokarin matsawa wasu daga cikin 'yan tawayen sun nuna damuwa game da taimakon da NATO take bayarwa.

Bugu da kari sama da 'yan gudun hijira dari biyu ne yawanci daga kasashen Afrika, kudu da hamadar sahara wadanda aka debe daga Misrata, yanzu sun iso zuwa garin Benghazi dake hannun 'yan tawaye.

Kasar Canada ta zama kasa ta baya bayan nan da ta amince da 'yan tawayen a matsayin wakilan jama'ar kasar Libya.