Masu zanga-zanga sun kara da 'yan sanda a Girka

Masu zanga-zanga sun kara da 'yan sanda a Girka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya ma an gudanar da makamantan wannan zanga-zangar a kasar

An samu tashin hankali a gaban Majalisar Dokokin kasar Girka, lokacin da masu zanga-zanga suka taru a daidai lokacin da take muhawara kan matakan gwamnati na tsuke bakin aljihu.

Masu zanga-zangar sun jefi 'yan sanda da duwatsu, wadanda suka mayar da martani da harba barkonan tsohuwa kan masu zanga-zangar.

'Yan sanda sun hana su zagaye ginin majalisar. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi kalaman batanci ga 'yan siyasar kasar ta Girka.

An dai shirya zanga-zanga kala-kala a fadin kasar a ranar Laraba - wadanda wasu kungiyoyi da suka hada da na 'yan kwadago suka shirya.

Ana kuma yajin aiki wanda ya shafi asibitoci da harkokin sufuri da kuma kafafen yada labarai.