Za'a kafa sabuwar gwamnati a Girka

Pira ministan Girka George Papandreou
Image caption Pira ministan Girka George Papandreou

Praministan kasar Girka, George Papandreou, ya yanke shawarar kafa sabuwar gwamnati, a wani yunkuri na ganin an aiwatar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati, kamar dai yadda masu bada bashi suka bukata.

Praministan na Girka ya sanar cewa, gobe Alhamis zai soma zaben majalisar ministocinsa, sannan ya nemi amincewar majalisar dokokin kasar.

Tun farko George Papandreou yayi tayin yin murabus, bayan da 'yan adawa suka ki goyon bayan shirinsa na rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa.

Yayin da ake cigaba da ja-in-jar siyasar, masu zanga zanga sun yi ta yin arangama da 'yan sanda a kan titunan Athens, babban birnin kasar.