Nijer: Majalisa ta bude muhawara kan sauyawa kasuwanni fasali

Taswirar Nijer Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Nijer

A Jamhuriyar Niger yau ne majalisar kasar ta bude zaman wata muhawara domin kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike a game da wasu matsaloli da ke kai hukumomin kasar ga rusa wasu kasuwanni ko tashoshin motoci domin canza masu fasali.

Makasudin wannan tattaunawar yan majalisar dai shi ne gano musabbabin korar wasu yan kasuwa daga wata tashar mota mai suna Tashar Walam a cikin Birnin Yamai.

Sai dai hukumomin kasar sunce ire iren wadannan matsaloli na faruwa ne ta hanyar kin aiki da dokokin kasar da wasu mutane ke yi kamar mayarda Hilayen haya mallakarsu.