Yakamata Turai ta kara taimakawa NETO

Sakatare Janar na kungiyar tsaron NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya shaidawa BBC cewa kasashen Turai dake cikin kungiyar na bukatar kara yawan kudaden da suke kashewa ta fuskar tabbatar dat tsaro.

A ranar Juma'ar da ta gabata, sakataren tsaron Amurka, Robert Gates, ya soki kasashen turai, kan yadda ba sa ba NATO gudunmawa mai tsoka.

Mr Fogh Rasmussen ya ce, kungiyar tsaron NATO na bukatar agaji fiye da a kowane lokaci.

Ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen Turai su dauki nauyin da ya rataya a wuyansu.