Fadar Shehun Borno ta fitar da sanarwa kan rikicin Boko Haram

A jihar Bornon Najeria Fadar Shehun Borno ta fitar da wata sanarwa ga manema labarai game da al'amuran da suka shafi matsalar tsaro a birnin Maiduguri da ma wasu sassa na jihar.

Sanarwar ta jaddada rashin jin dadinta kan abinda ta ce,"boyewar da wasu ke yi karkashin sunan kungiyar Boko Haram suna yada farfagandar tayar da hankulan jama'a tare da aikata ba daidai ba".

A kwanaki biyun da suka gabata ne dai aka samu wasu kasidun sanarwa ga manema labarai masu dauke da kalaman da suka nuna cewar kungiyar Jama'atu Ahlus Sunna Lidda'awati Wal Jihad da ake kira Boko Haram ta ce, ba za ta daina kaddamar da hare hare a birnin Maiduguri da ma wasu sassan jihar ba, har sai mai martaba Shehun Bornon Alhaji Abubakar Umar Garbai El Kanemi da gwamnan jihar Bornon Kashim Shettima sun sauka daga mukamansu.

Sannan kuma an gurfanar da tsohon gwamnan jihar Ali Modu Sheriff da wasu kusoshin gwamnati a gaban kotu.