Jama'a sun yi zanga-zanga a Sakkwato saboda rashin lantarki

Taswirar Nijeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Nijeriya

Jama'ar wata unguwa dake birnin Sakkwato a Najeriya sun gudanar dawata zanga-zanga a harabar ofishin kamfanin samar da wutar lantarki na kasa domin nuna rashin amincewarsu da rashin samun wutar lantarki.

Matsalar samar wa jama'a abubuwan more rayuwa da suka hada da wutar lantarkin dai, matsala ce da wasu ke ganin ta zama ruwan dare a kasar, duk kuwa da ikirarin da hukumomi ke yi cewar suna yin iya kokarinsu wajen kyautata lamura.