Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai hari

Motoci sun kone kurmus Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin babbar barazana ce ga tsaron kasa

Kungiyar nan ta Ahlus Sunna Lil-da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram ta tuntubi sashen Hausa na BBC in da ta bayyana cewar ita ce ke da alhakin kai wannan hari na birnin Abuja.

Kamar yadda wani mai magana da yawun kungiyar, wanda ya kira kansa Abu Zaid ya bayyana, sun kai wannan hari ne, saboda irin kalaman baya bayan nan da suke zargin sufeto Janar na 'yan sandan Nigeria, Alhaji Hafiz Ringim yayi akan kungiyarsu.

Haka nan kuma mai magana da yawun kungiyar ya ce Kungiyar su ta na nisanta kanta da wasu mutane da a baya bayan nan ya ce suna fitar da sanarwa a madadin kungiyar ta Boko Haram.

Da ma dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce tana zargin kungiyar nan ta Boko Haram da kai harin bom a hedikwatarta dake Abuja babban birnin Najeriya.

'Yan sandan sun ce wanda ake zargi da kai harin bam din ya yi kokarin shiga cikin jerin gwanon motocin babban Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriyar ne a lokacin da ya ke shiga hedikwatar 'yan sandan.

Nan take ne kuma aka karkatar da akalar motar ta sa zuwa wurin da aka kebe domin ajiye motocin baki, inda kuma a nan ne bam din ya tashi.

Tashin bam din mai karfin gaske ya yi sanadiyar mutuwar mutane, da jikkata wasu da ma kona motoci da dama.

Ita dai hedikwatar 'yan sandan Najeriya tana a wani yanki ne dake kasa da kilomita guda daga fadar shugaban kasa ta Aso Rock.