Sarkozy ya yi hannunka mai sanda ga kasashen Turai

Girka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An shafe ranar Laraba ana zanga-zanga a Girka

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy ya yi kira ga shugabannin kasashen Turai da su gaggauta cimma yarjejeniya kan hanyar da ta fi dacewa a taimakawa kasar Girka.

Ya kuma ne da a bullo da wata hanyar da za a kare darajar takardar kudin Euro.

Mr Sarkozy na yin hannunka mai sanda ne game da bambancin ra'ayin da aka samu kan shawarar ceto tattalin arzikin Girka cikin shekaru uku masu yawa.

Kasashe da dama ciki har da Jamus sun nemi bankunan dake rike da kadarorin gwamnatin Girka da su ma su bada tasu gudummawar.

Sai dai Faransa da sauran kasashe na nuna damuwar cewa idan hakan ta faru, za a iya bayyana Girka, a matsayin wadda ta guje ma biyan bashin da ake bin, wanda kuma hakan na iya haifar da wata matsalar da zata yi illa ga tsarin tattalin arzikin duniya.