Gagarumin garambawul a gwamnatin Girka

Sabon ministan kudin kasar Girka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabon ministan kudin Girka Evangilos Veni-zelos

Gagarumin sauye-sauyen da akai a majalisar ministocin kasar Girka ta kai ga samar da sabon ministan kudin kasar a wani kokari na samun karin goyan bayan siyasa.

Fira Minista Goerge Papandreou na neman samun goyon baya ne a cikin gida akan matakan tsuke bakin aljihun da masu bada bashi na kasa da kasa suka bukaci ayi.

Kakakin gwamnatin Girkan ne ya bayyana sunayen da sabuwar majalisar zartarwar kasar ta kunsa.

Sabon ministan kudin, Evangilos Veni-zelos wanda ya dade yana sukar Fira Ministan kasar Goerge Papandreou, ya taba rike ministan tsaron kasar.

Sauye-sauyen sun zo ne bayan zanga-zangar da akai tayi a kasar dama kin amincewar wasu 'yan adawa da sabon shirin rage kudaden da gwamnati ke kashewa da ma karin kudaden haraji.