Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Yoyon fitsari ga masu jego

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Wasu mata masu fama da yoyon fitsari na jiran gan ni likita a Najeriya

Wani bincike da Farfesa JP Neilson ya gabatar ya nuna cewa haihuwar dake zuwa da gardama ita ce kashi daya cikin biyar na manyan dalilan dake janyo mace-macen mata masu juna biyu a gurin haihuwa.

Binciken wanda aka wallafa a Mujallar kiwon lafiya ta Burtaniya da jami'ar Oxford ke wallafawa ta nuna cewa haihuwar da ke zuwa da gardama wata babbar matsala ce dake sandiyyar mutuwar mata masu juna biyu ko a yayin haihuwa ko kuma nakasa su.

Haka kuma ta kan janyo nakasar da su a kasashe masu tasowa.

Makalar ta bayyana cewa yawan mace-macen mata masu juna biyu a sanadiyyar nakudar da tazo da gardama ko yagewar mahaifa ya kama daga kashi hudu cikin dari zuwa kashi 70 cikin dari na dukkan mace-macen mata masu juna biyun da ake samu.

Hakan kuma ya kai kimanin kashi 410 cikin kowane haihuwa dubu dari da 'ya'ayan suka zo a raye.

Adadin dai acewar makalar na nufin a kasashe da dama yawaitar mace-macen mata masu juna biyu ta wannan hanyar abu ne da a yau ya zama ruwan dare kamar yadda yake a shekaru 30 da suka shude.

A Najeriya ma dake nahiyar Afrika ana samun masana dake nazari a kan cutar ta yoyon Fitsari.

Dr Adamu Isa likita ne a fannin yoyon fitsari da ke tare da wata kungiya dake kula da masu yoyon fitsari wacce hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka USAID ke tallafawa.

Kuma a shirin Haifi Ki Yaye da BBC Hausa na wannan makon, ya yi bayani dalla-dalla kan cutar.