Tsokacin masana kan harin hedkwatar 'yan sanda

Wurin ajiye motoci na Gidan Louis Edet Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wurin ajiye motoci na Gidan Louis Edet bayan harin

A Najeriya, harin bom din da kungiyar nan ta Ahlus Sunnah lid Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta ce ita ta kai a hedkwatar 'yan sanda ta kasar, wato Gidan Louis Edet a Abuja, ya kara fitowa fili da babban kalubalen da kasar ke fuskanta ta fuskar tsaro, inda tashe-tashen bama-bamai ke neman zama tamkar ruwan dare.

Jami'ai dai sun ce wanda ake zargi da kai harin bam din ya yi kokarin shiga cikin jerin gwanon motocin Sufeto Janar na 'yan sandan kasar ne a lokacin da ya ke shiga hedkwatar 'yan sandan.

Nan take ne kuma aka karkatar da akalar motar tasa zuwa wurin da aka kebe domin ajiye motocin baki, inda kuma a nan ne bam din ya tashi.

Tashin bam din mai karfin gaske ya yi sanadiyyar mutuwar mutane, da jikkata wadansu da ma kona motoci da dama.

Ita dai hedkwatar 'yan sandan Najeriya tana wani yanki ne dake kasa da kilomita guda daga fadar shugaban kasa ta Aso Rock.

Hakan kuma ya sa wadansu 'yan kasar na cewa matsalar tabarbarewar tsaro a kasar a yanzu ta kai wani mummunan matsayi.

A cewar wani tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ’yan sandan (DIG), Alhaji Bala Uba Ringim, wanda ya ce sha’anin tsaro abu ne na kowa da kowa ba ’yan sanda kawai ba, “abin dai sai dai a ce ‘inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un’.”

To ko wadanne hanyoyi za a bi domin fita daga wannan yanayi?

“Kamar wannan abin da ya faru”, in ji Alhaji Bala Uba Ringim, “idan mutanen Naija Delta sun yi rigima an zauna da su an daidaita, don me su wadannan ba za a zauna da su a daidaita ba?

“Mutane ne [wadanda] suke ganin an musu ba daidai ba; to a zauna da su [a tambaye su]: ‘me aka yi muku ba daidai ba?’ [Idan suka ce] ‘Kaza aka yi mana ba daidai ba’, [sai] a gyara”.

Dangane da yadda za a kawo gyaran kuwa, tsohon jami’in rundunar ’yan sandan cewa ya yi:

“Ni ina ganin dole ne da gwamnati, da hukumar ’yan sanda, da jama’a su hadu, su zauna, su samo yadda za a warware al’amarin nan....

“A ba [’yan sanda] kayan aikin da ya dace a kuma taimaka musu; a kuma fadakar da mutane—duk yadda na ke so in kare ka, ka fi so ka kare kanka; to idan ba a fadakar da kai ba yadda za ka kare kanka, ni ba zan iya kare ka ba”.

A yanzu dai irin wannan al'amari na fashewar bama-bamai ko kuma gano su kafin su fashe ya zama wani babban kalubale ga jami'an tsaron kasar, wadanda duk da abin da ke faruwa suke cewa suna iya kokarin su don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'ar kasar.

Karin bayani