Karin zanga zangar nuna adawa a Syria

Dubban jama'a a Syria sun gudanar da zanga zangar nuna kyamar gwamnatin shugaba Bashar al-Assad, a garuruwa da birane daban daban na kasar.

Kafar yada labaran gwamnati ta ce an harbi 'yan sanda da dama, inda daya ya rasa ransa.

Wasu rahotanni daga 'yan gwagarmaya, wadanda ba a tabbatar da su ba, sun ce akalla masu zanga zangar goma sha shidda ne jami'an tsaro suka harbe har lahira, a wurare daban daban, sai dai lamarin ya fi muni a Homs.