Zaman Zulumi a Abuja bayan harin bam.

A Najeriya, mazauna birnin Abuja na ci gaba da zaman dar-dar tun bayan harin bama-baman da aka kai a hedkwatar rundunar 'yan sanda ta kasa, a shekaranjiya, Alhamis.

Duk da cewa rundunar 'yan sandan ta ce za ta ci gaba da kokarinta na kare rayukan jama'ar kasar, wasu mazauna birnin na Abuja, sun ce a yanzu suna kaurace wa wurare da dama, musamman wuraren da ke da cinkoson jama'a don gujewa fadawa tarkon irin wadannan mahara.

Kungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haram dai ta yi ikirarin cewa ita ta kai harin, wanda ya haddasa mutuwar mutane akalla shidda.