An kai harin kunar bakin wake a Kabul

Harin kunar bakin wake a Kabul Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin kunar bakin wake a Kabul

An kai harin kunar bakin wake a kan wani Ofishin 'yan sanda da ke kusa da fadar shugaban kasa a Kabul, babban birnin Afghanistan.

Jami'an tsaro hudu da fararen hula biyar ne suka rasu a harin.

Wani da ya shaida al'ammarin, ya ce abubuwa uku ne suka fashe.

A bangare daya kuma, wasu jami'an 'yan sanda biyu sun samu raunuka a lokacin da suka yi yunkurin kwance wani bam da aka dana a bakin hanya a birnin na Kabul.

A can lardin Ghazni na gabashin kasar kuwa, masu tayar kayar baya ne suka kai hari a kan wasu ayarin motoci biyu dake kai kaya ga sojojin NATO, inda suka hallaka masu gadi 4.