'Yan bindiga sun bude wuta a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno a Nijeriya na cewa, wasu 'yan bindiga sun bude wuta kan wasu mutane dake wasan karta, har an samu asarar rayuka da kuma jikkata jama'a.

Lamarin ya auku ne a unguwar Gomari-Airport, dazu da maraicen nan.

Duk da kasancewar ba a shaida maharan ba, amma harin ya yi kama da irin wanda 'yan Kungiyar nan ta Ahlus Sunna Lil-da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram ke kaiwa.

Yunkurin da BBC ta yi domin samun karin bayani kan harin daga rundunar 'yan sanda, ya ci tura, sai dai wata majiyar tsaro ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa mutane biyu ne suka mutu, baya ga wadanda aka jikkata.