'Yan fashi sun kashe mutane a Onitsha

Rahotanni na cewa, an gano gawawwakin mutane akalla sha uku a wani wuri dake birnin Onitsha na kudu maso gabashin Najeriya.

Sai dai 'yan sanda sun ce, gawa daya kawai aka samu, amma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, gawawwakin sun ma kai ashirin.

Ana dai zaton 'yan fashi da makami ne suka hallaka mutanen da aka gano gawawwakin nasu.

Fashi da makami dai na daya daga cikin manyan matsalolin tsaro da ake fama da su a Nijeriya, musamman a sashen kudu maso gabashin kasar.