Sammacin kama Alhaji Moussa Dan Foulani

Taswirar Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin Nijar ta bada sammacin kama wani na hannun daman tsohon shugaban kasar, Malam Mamadou Tanja.

A ganawar da ya yi yau da 'yan jarida a Yamai, ministan shari'a, Malam Marou Amadou, ya ce su na zargin Alhaji Mousa Dan Foulani, wanda har illa hamshakin dan kasuwa ne, da aikata almundahana ta biliyoyin kudin CFA a Nijar, dangane da wasu kwangilolin da suka hada da samar da takin zamani.

Malam Marou Amadou ya ce sun sanar da kungiyar 'yan sanda da kasa da kasa, watau Interpol don cafke Alhaji Moussa Dan Foulanin, wanda yanzu haka yake Tarayyar Najeriya, ta kuma tesa keyarsa zuwa Nijar din.

Sai dai a kwanakin baya, Alhaji Mousa Dan Foulanin ya ce, idan aka bi diddigi, shi ne ma ke bin gwamnatin Nijar din bashin kudade.