Yau ce ranar bikin yan gudun hijira ta duniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu yan gudun hijira da suka fito daga Syria

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar 'yan gudun hijira ta duniya.

Bincike dai ya nuna cewa akwai 'yan gudun hijira sama da miliyan goma sha shida a duniya, akwai kuma kimanin mutane miliyan ashirin da shida a sassan daban daban na duniya wadanda suka rasa muhallansu.

Tun bayan hambaradda shugaban kasar Tunisia Zine al-Abidini Bin Ali a watan Janairu, 'yan gudun hijira fiye da dubu arba'in ne daga Arewacin Afrika suka iso tsibirin Lampedusa dake kasar Italiya, inda suke neman hanyoyin kyautata rayuwarsu.

To a Najeriya ma dai, mutane da dama ne suka rasa muhallansu, sakamakon tashe -tashen hankulan da suka auku bayan zaben shugaban kasar a sassa daban daban na kasar.

A jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, yanzu haka dubun dubatar jama'a ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijirar da gwamnatin jihar ta tanadar, bayan da mutanen suka rasa muhallansu sakamakon rikicen rikicen bayan zaben .