'Yan tsirari ne ke tada hankali a Syria - al-Assad

Assad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Assad ya zargi masu zagon kasa da shirya zanga-zanga

Shugaban Syria Bashar al-Assad ya dora alhakin zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin da ake yi kan wadanda ya kira "'yan tsiraru" masu yunkurin zagon kasa.

A jawabi na uku da ya yi tun bayan fara zanga-zangar, ya ce Syria za ta shawo kan bukatar jama'arta ta neman sauyi amma wasu 'yan tsiraru na amfani da wannan damar wajen tayar da hankali.

Ya yi alkawarin tattaunawa kan makomar kasar, yana mai kira ga wadanda suka yi kaura zuwa Turkiyya da su dawo gida.

Sai dai ya ce mutuwar masu zanga-zangar abin bakin ciki ne ga kasar da kuma shi kansa.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce a kalla mutane 1,300 ne aka kashe yayin da aka tsare wasu 10,000 a watanni ukun da aka shafe ana zanga-zangar.

An kuma kashe sojoji da 'yan sanda fiye da 300. Gwamnati ta dora alhakin kisan kan kungiyoyin 'yan ta'adda.

'Barna'

Da ya ke magana ga magoya bayansa a jami'ar Damascus, Mr Assad ya nuna takaici kan asarar rayukan da aka yi a lokacin zanga-zangar.

Sai dai ya ce masu yunkurin zagon kasa da suka batawa kasar suna a idon duniya, dole ne a mai da su saniyar ware.

Ya kara da cewa: "abin da ke faruwa yanzu ba shi da alaka da neman sauyi, kawai barna ce da wasu mutane suka shirya."

"Ba zai yiwu a samu ci gaba idan ba zaman lafiya ba, kuma ba za a samu sauyi ba ta hanyar barna da fada."

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Har yanzu ana ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati

Sai dai shugaban ya ce za a kafa kwamitin tuntuba domin kawo sauye-sauye da kuma wani kwamitin da zai duba tsarin mulkin kasar.

A bangare guda kuma, dubban jama'ar da suka kauracewa matakin soji a Arewacin kasar na neman mafaka a kasar Turkiyya.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun ce sojoji sun datse garin Bdama, inda ake samar da kayan agaji ga wadanda suka tsere daga garin Jisr al-Shugour.

'Majalisar Koli'

Jawabin na shugaba Assad ya zo ne kwanaki guda bayan da 'yan adawa suka kafa Majalisar koli da za ta jagorance su a yunkurin da suke yi na kawar da shi.

"Mun bayyana kafa Majalisar Koli domin jagorantar zanga-zangar Syria, wacce ta hada dukkan al'ummar kasar da kuma 'yan siyasa na ciki da wajen kasar, " kamar yadda mai magana da yawunta Jamil Saib ya gayawa manema labarai a kan iyakar kasar da Turkiyya.

Majalisar ta nemi "jama'a da su bada hadin kai a ko'ina a Syria domin tabbatar da burin da ake da shi na kifar da gwamnatin Syria da kuma gurfanar da ita a gaban shari'a", a cewar Saib.

Fiye da 'yan gudun hijira 10,000 ne suka tsallaka zuwa Turkiyya, kuma mahukunta a Turkiyya sun ce wasu karin 10,000 na neman mafaka a bangaren Syria.

Raka al-Abduh, dan shekaru 23, ya shaidawa AFP cewa danginsa sun tsere daga garin Bdama ranar Asabar amma da ya koma ranar Lahadi domin samun biredi.

Sai ya ga babu kowa a garin.

"Sojoji sun rufe gidan biredi taya tilo da ya rage a garin. A yanzu ba ma iya samun biredi."

An kuma samu karin zanga-zanga a garuruwan Hama da Homs da Latakia da Deir al-Zour da Madaya da kuma wasu sassa na Damascus, a cewar masu fafutuka.