Kuri'ar amincewa da matakan gwamnatin Girka

Girka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ministocin kudi na kasashen da ke amfani da Euro bayan kammala taronsu

Ana gudanar da zanga-zanga a kasar Girka a daidai lokacin da Majalisar kasar za ta kada kuri'ar amincewa kan shirin gwamnatin kasar na tsuke bakin aljihu.

Ana bin kasar makudan kudade, kuma kasashen da ke amfani da kudin Euro sun ce za su kara tallafawa kasar ne kawai idan ta kara daukar matakan tsuke bakin aljihu.

Kungiyoyin kwadago da dama ne suka shiga yajin aiki domin nuna adawa da shirin na gwamnatin ta Girka.

A makon da ya wuce 'yan kasar ta Girka suka gwabza da 'yan sanda a gaban ginin Majalisar Dokokin, bayan wani zama na yunkurin amincewa da tsarin.

Akwai dai yiwuwar Majalisar ta amince da sabon tsarin da dan karamin rinjaye.

Tuni dai Fira Ministan kasar ya yi gagarumin garambawul ga Majalisar ministocinsa, inda ya sauya ministan kudi.

Masu sharhi na ganin Fira Ministan ya dauki matakin ne domin samun goyon bayan sauran jam'iyyu a Majalisar.

A baya ma dai kasar ta dauki irin wadannan matakai na tsuke bakin aljihu, amma masu bada lamuni sun shaida mata cewa akwai bukatar kari.