Mutane ashirin da biyu sun hallaka a Iraqi

Mutane ashirin da biyu sun hallaka a Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tuni dai jami'an tsaro suka killace wurin da harin ya faru

Hukumomi a tsakiyyar Iraqi sun ce akalla mutane ashirin da biyu ne suka hallaka a wani harin bam a birnin Diwaniya mai nisan kusan kilomita dari da hamsin da Bagadaza babban birnin kasar.

Sun ce mutane da dama sun samu raunuka a lokacin da wasu motoci biyu makare da bama-bamai suka tashi kusa da gidan gwamnan lardin.

Hakazalika da dama daga cikin mutanen da abun ya shafa 'yan sanda ne.

Sai bai babu wani cikakken bayanai akan ko gwamnan ya samu rauni.