Uwargidan Obama ta ziyarci Nelson Mandela

Uwargidan Obama ta ziyarci Nelson Mandela
Image caption Wannan ne karo na farko da Michelle Obama ke ziyara a Afrika

Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama tare da mutan gidan, sun kai wata ziyarar girmamawa ga tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela.

Wani hoto da Gidauniyar Nelson Mandela ta fitar, ya nuna Mandela dan shekaru 92, cikin koshin lafiya - yana zaune a kan kujera kusa da Mrs Obama, dauke da biro yana shirin sa hannu kan wani littafi na tarihin rayuwarsa. Mandela yana sanye ne da daya daga cikin rigunan da ya saba sanyawa, mai maballaye daga sama har kasa.

Wannan ce haduwa ta farko tsakanin uwargidan shugaban Amurka bakar fata na farko da kuma tsohon dan gidan fursuna wanda ya zamo bakar fata na farko da ya shugabanci kasarsa. Ya'yan Mrs Obama, Malia, 'yar shekara 12, da Sasha, 'yar shekara 10, da kuma babarta, Marian Robinson, suna kallon wasu kayayyakin Mandela ne a cibiyarsa ranar Talata, lokacin da ya bayyana cewa zai gana da su a gidansa da ke birnin Johannesburg.

Ta samu kyakkyawar tarba

Uwar gidan shugaban Amurkan ta shafe mintina 20 tare da Mandela da kuma matarsa Graca Machel.

Mandela, wanda ya sauka daga kan karagar mulki bayan wa'adi daya a 1999, ba a fiya ganinsa a bainar jama'a sosai ba.

Ya yi fama da rashin lafiya kuma an kwantar da shi a asibiti na wani dan lokaci a watan Janairu.

Mrs Obama ta kuma samu kyakkyawar tarba lokacin da ta yi jawabi ga mambobin kungiyar mata ta Young African Women Leaders Forum.

Michelle Obama tare da iyalanta sun kammala ayyukansu a ranar Talata tare da ziyarar gidan tarihi na abubuwan da suka faru a lokacin mulkin wariyar launin fata.

Ranar Litinin Mrs Obama ta fara ranar ziyarar mako guda a kasashen Afrika ta Kudu da kuma Botswana.