'Yansanda na yin taro kan sha'anin tsaro a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya na yin taro a kan tabarbarewar harkokin tsaro a kasar.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ake fama da hare-hare da kuma tashin bama-bamai a wasu yankunan arewacin kasar.

Kasa da mako guda kenan da kungiyar nan ta Ahlissunna Lidda'awati Wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta kai hari a hedkwatar 'yan sandan da ke Abuja, inda mutane takwas suka hallaka.

Ko a jiya ma, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a caji ofis da kuma wani banki a garin Kankara na jahar Katsina, inda suka kashe kimanin mutane bakwai.

Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum, da ma wasu shugabannin al'uma a Najeriya na ganin cewa, yin sulhu da kungiyar Boko Haram, shi ne zai kawo karshen hare-haren da ake zargin kungiyar na kaiwa.

A makonnin baya gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya fito yayi tayin neman sulhun, sai dai wasu 'ya'yan kungiyar sun yi watsi da hakan.