Shugaba Asad ya daina daukar wayata: in ji Ban ki Moon

Ban Ki Moon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ban Ki Moon ya koka sosai kan Syria

Sakatare janarar na Majalisar dinkin duniya Ban ki Moon yayi amfani da wata hira da yayi da BBC domin sake yin kira ga kasar Syria data bada dama ga masu bincike da masu ayyukan agaji su shiga cikin kasar .

Yayinda yake magana bayan an sake zabarsa a matsayin sakatare janarar na Majalisar dinkin duniyar, Mr Ban yace ya damu matuka game da yadda ake keta hakkin bil adama a kasar Syrian, kasar da aka shafe wata da watanni ana gudanar da zanga zanga da kuma asarar daruruwan rayuka.

Ya ce shi yasa yake ta magana da Shugaba Asad, amma ya ce shugaba Asad ya daina daukar wayarsa idan ya kira a yan kwanakin da suka wuce.

An dai sake nada Mr Ban ne a matsayin sakatare janarar na Majalisar dinkin duniya ta hanyar tafi inda wakilan kasashen duniya suka nuna goyon bayansu ta hanyar tafi a maimakon kada kuria.