Ambaliyar ruwa a Kano

A jahar Kano mutane 24 ne suka rasa rayukansu, inda wasu da dama kuma suka jikkata, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren jiya.

An shafe kimanin sa'a guda ana sheka ruwan saman.

Wajejen gidaje 30 ne suka ruguje sakamakon ruwan saman, kuma an yi hasarar dukiya mai yawa.

Wasu shaidu sunce yau fiye da shekara talatin kenan rabonsu da ganin ruwan sama irin wannan.

Wannan matsalar ambaliyar dai ta zo ne a dai dai lokacin da masana ke wani taro a Abuja, akan yadda za'a tunkari bala'in ambaliyar ruwa a kasashen yammacin Afirka.