Tattaunawa kan kasar Girka

Tutar kungiyar Tarayyar Turai
Image caption Za a gudanar da taro kan Girka

Nan gaba a yau Alhamis ne shugabannin tarayyar Turai za su hallara a birnin Brussels don yin taron koli, inda ake sa ran za su tattauna kan matsalar tattalin arzikin Girka.

Mahalarta taron, za su kuma tattauna a kan makomar kudin bai-daya na euro.

Ana dai tunanin shugabannin na Tarayyar Turai za su jaddada kudurinsu na bayar da kariya ga kudin na bai-daya.

Sai dai ko da yake an shirya taron ne don magance matsalar tattalin arzikin da yankin ke fuskanta, abin da shugabannin za su iya yi takaitacce ne, yayin da suke jiran ganin ko majalisar dokokin kasar ta Girka za ta amince da matakan tsuke-bakin-aljihu.