'Yansanda sun yi tayin sasantawa da Boko Haram

'Yan sandan Najeriya
Image caption Ko 'yan Boko Haram za su amsa kira?

Rundunar Yansandan jihar Borno a Nijeriyar ta fitar da wata sanarwa ta tayin neman yin sulhu da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal jihad da aka fi sani da Boko Haram.

Har ila a yau sanarwar Rundunar Yansandan nuni da cewa motocin sulken da gwamnatin jihar Bornon ta bayar gudummawa a makon jiya ba an yi hakan ne da nufin yin illa ga wani mutum ko wata kungiya ba, illa kawai domin kokarin kare rayuka da dukiyoyin jama'a. Kungiyar ce dai ake dangantawa da galibin hare-hare na bindiga da bama-bamai a sassa da dama na arewacin Nijeriya, musamman mai dai a birnin Maiduguri.

A baya dai, kungiyar ta Boko Haram ta yi watsi da tayin sulhu tana cewa, an sha ma ta alkawurra ana karyawa.