Shugabannin Nato sun bi sahun Amurka kan Afghanistan

Obama
Image caption Obama ya ce zai janye sojojin Amurka dubu talatin

Shugabannin kasashen kungiyar tsaro ta Nato sun bayyana shirin janye sojojinsu daga Afghanistan bayan da Amurka ta ce za ta janye sojinta dubu talatin daga can.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya ce dakarun kasar dubu hudu da ke Afghanistan za su janye a irin wannan tsarin.

Itama Jamus ta ce za ta fara rage adadin dakarunta a kasar nan gaba a cikin shekaran nan.

Yayin da Burtaniya ta ce dakarunta ba za su kara shiga harkokin yaki a kasar ta Afghanistanba nan da shekaru hudu masu zuwa.

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai, ya yi maraba da da matakin shugaba Obaman ya dauka na janye sojojin Amurka daga kasar nan da watanni 15 masu zuwa.

Sai dai kungiyar Taliban ta yi watsi da sanarwar, tana mai kira da su janye nan take.

Karin bayani