An sabunta: 23 ga Yuni, 2011 - An wallafa a 10:11 GMT

Ra'ayi Riga: Ranar tunawa da zaurawa ta duniya

Ranar zaurawa ta duniya

Wannan ne karo na farko da aka ware ranar domin tunawa da Zaurawan

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 23 ga watan Yuni domin zamo wa rana ta farko da za a dinga tunawa da matan da mazajensu suka rasu.

Shin wanne irin hali matan suke samun kansu a ciki?

Suna samun irin taimakon da ya kamata ko kuma a'a?

Ta yaya za a taimaka musu?

Wannan shi ne abin da za mu tattauna a shirinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon:

Domin shiga cikin shirin sai ku aiko mana da ra'ayoyinku ta adireshinmu na email, wato hausa@bbc.co.uk, ko ta lamba 44 77 86 20 20 09.

Ko kuma ta dandalin mu na muhawara, wato BBCHausa Facebook, wanda za ku iya samu a shafinmu na internet, wato bbchausa.com.

Ko kuma ta hanyar cike wannan gurbin da ke kasa:

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.