'Yan kwallon Libya sun goyi bayan 'yan tawaye

'Yan kwallon Libya sun sauya sheka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan kwallon Libya, Juma Gtat

Wasu fitattun 'yan wasan kwallon kafa su goma sha bakwai a Libya sun ba da sanarwar sauya sheka zuwa bangaren 'yan tawaye.

A cikinsu har da 'yan wasa hudu na babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar, wadanda suka hada da mai tsaron gida na kungiyar , Juma Gtat, da mai horar da kulob mafi girma a Turabulus, wato Al-Ahly, Adel Bin Isa.

Da ya ke zantawa da BBC, Juma Gtat ya yi kira ga Kanar Gaddafi ya kyale 'yan Libya su samar da kasa mai 'yanci.

Kocin kulob din na Turabulus kuwa cewa ya yi, ya gaji da jin batun Gaddafi.

Ya kara da cewa: ''Ina so na wayi gari gobe ba tare da ganin Gaddafi a kasa ta ba''.

Wannan sauya sheka da 'yan kwallon na Libya suka yi dai, wata gagarumar nasara ce ga 'yan tawaye ta fuskar farfaganda.