Sanusi ya yi karin haske kan 'Bankin Musulinci' a Najeriya

Karin haske game da 'bankin Musulinci' a Najeriya
Image caption Sanusi Lamido Sanusi

Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya yi karin haske dangane da cece-kucen da wasu ke yi a kasar game da matakin da bankin ya dauka na baiwa Bankin Ja`iz amincewa domin fara gudanar da harkokin banki irin na Musulunci.

Gwamnan Babban Bankin Najeriyar, Sanusi Lamido Sanusi, ya ce matakin da Babban Bankin ya dauka bai saba wa doka ba.

Ya kara da cewa, koda a kasashe irin su Burtaniya, da Faransa, da Italiya, inda galibin 'yan kasar ba musulmai ba ne, ana gudanar da tsarin banki na addinin Musulinci.

Malam Sanusi ya ce mutanen da ke sukar tsarin bankin musulincin na yin hakan ne ko dai saboda basu da masaniyar tsarin, ko kuma domin kiyayyarsu ga addinin Musulinci.