An kashe mutane sha biyu a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Syria na cewa mutane akalla sha biyu aka kashe a zanga zanga ta baya-baya dake neman a sauke Shugaba BasharAl-Assad.

Dubban mutane ne suke sake hawa kan tituna bayan sallar Juma'a a garuruwa da manyan biranen kasar, inda jami'an tsaro suka maida martani ta hanyar harba barkonon tsohuwa da bude wuta a kan masu zanga zanga.

Masu fafutukar kare hakkin jama'a, sun ce an bindige mutane biyar har lahira a Kiswah, kusa da birnin Damascus, lokacin da suke fitowa daga sallar Juma'a, da kuma a birnin Homs.