Sojin Syria sun nufi kan iyakar Turkiyya

Sojin Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijira daga Syria suna kara nufa Turkiya

Dakarun Syria da da tankunan yaki suna cigaba da motsawa a arewa maso yammacin kasar kusa da kan iyaka da Turkiyya da kuma garin Al-Quseir kusa da iyaka da Lebanon.

Ana dai ci gaba da gudanar da zanga zanga a wasu sassa na kasar:

Masu fafutuka sun ce an tsare jama'a da dama.

Dubunnan 'yan kasar ta Syria sun tsere zuwa Turkiyya da Lebanon a 'yan makonnin nan domin kaurace wa durfafar da sojoji suke yi wa masu zanga-zangar nuna kyamar gwamnati.

Haka kuma an kasha daruruwan mutane a zanga-zangar da aka kwashe makonni ana yi.