Shugabannin Afrika na taro kan rikicin Libya

Shugaba Zuma da Shugaba Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Zuma da Shugaba Gaddafi

Shugabannin kasashen Africa na wani taro akan Libya, a Afrika ta kudu, a wani yunkuri na shiga tsakani a rikicin Libyar.

Shugaban Africa ta Kudu Jacob zuma, wanda ya ziyarci Trablis, babban birnin Libya a watan jiya ne ke jagorantar tattaunawar.

Kungiyar tarayyar Afrika ta AU dai ta ce bata goyon bayan hare-haren da NATO ke kaiwa a Libya, yayin da kuma tace Gaddafi ya ajiye mulki cikin mutunci.