Sakamakon bincike a kan ciwon suga

Image caption Karuwar kiba na haddasa ciwon suga

Binciken da aka gudanar a kan ciwon suga a fadin duniya ya gano cewa daga shekarar 1980 zuwa yanzu yawan mutanen da ke dauke da cutar ya kai kusan miliyan dari uku da hamsin.

Daya daga cikin wadanda suka wallafa rahoton, Farfesa Majid Ezzati, ya ce ciwon suga na dab da zama ciwon da ya fi yiwa harkar kiwon lafiya a duniya shiga-hanci da kudundune.

Ciwon suga dai kan lalata koda ya kuma haddasa makanta.

Binciken ya kuma gano cewa karuwar al'umma da kuma karuwar wadanda suka manyanta a cikin al'ummar da ma karuwar kiba su ne suka haddasa karuwar cutar.