'Yan bindiga sun kai hari gidan makoki a jihar Borno

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno

A jihar Borno arewacin Najeriya rahotanni na cewa wasu 'yan bindiga sun bude wuta a wurin taron zaman makoki dake garin Gamborun Ngala yankin Karamar Kukumar Ngala inda mutum guda ya rasa ransa yayin da wasu suka jikkata.

Taron zaman makokin da 'yan bindigar suka budewa wutar na wani tsohon mataimakin shugaban Karamar Hukumar ta Ngala ne wanda wasu 'yan bindigar suka hallaka da karfe takwas na daren shekaranjiya a kofar gidansa.

Ko a safiyar yau din ma a garin na Gamborun Ngala sai da wasu 'yan bindigar suka harbe wani mai sayar da katako har lahira, lamarin da yanzu haka ya sanya zullumi a tsakanin mazauna garin.