Janar Buhari ya ce adalci ne zai magance matsalar tsaro

Dan takarar Shugaban Kasar Najeriya a zaben da ya gabata na shekarar 2011, Janar Muhammad Buhari ya bayyana cewa adalci shi ne kadai zai iya magance matsalar tsaron da ake fama da ita a Kasar.

Janar Buhari yayi wannan tsokaci ne a London, bayan kwamitin yakin neman zaben Shugaban Kasa na jam'iyyar CPC ya gabatar da wasu kasidu kan irin kalubalen da aka fuskanta a zaben da ya gabata a Cibiyar nazarin harkokin Kasashen waje ta Chatham House.

Janar din ya fara yin tsokaci ne game da matsalar tsaron da ake fama da ita a sashen arewa maso gabashin Najeriya.

Ya dai bayyana cewa muddin ba ayi wa al'ummar Kasa adalci ba, to abubuwa ba za su tafi yadda ya kamata ba.