'Yan tawayen Libya na nufar birnin Tripoli

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan tawayen dake adawa da shugabancin Kanar Gaddafi a Libya sun nausa zuwa kimanin mil talatin kwatankwacin kilomita hamsin daga babban birnin Tripoli.

'Yan tawayen da suka yada zango a tsaunukan Nafusa, wadanda suma bangare ne na dakarun 'yan adawar hadin gwuiwa a kasar, na gab da shiga birnin Tripoli.

Da fari suna boye ne a tsaunukan, amma yanzu sun sauko kasa, inda suka buya a surkukun dajin dake kasan tsaunukan.

Da yake dakarun Kanar Gaddafi na da makaman da ake amfani da su ta kasa, wadanda ke zuwa nisan wani zango, sun yi ta faman harba su.

Sai dai duk da haka, wadannan 'yan adawar na da hanyoyin samun makamai wanda dakarun Kanar Gaddafi ke ta kokarin ganin sun katse hanyoyin.

Wurin da 'yan tawayen Libyan ke hara dai shine birnin Tripoli, wanda kuma idan har ba gwamnatin Kanar Gaddafi ce ta rushe ba, da wuya su iya kai gaci.

Sai dai 'yan tawayen sun ce suna ci gaba da kutsawa sabbin yankuna.

Kakakin dakarun 'yan tawayen, ya ce, ko a jiya ma sai da suka tabka kazamin bata- kashi a wajen birnin Bair al-Ghanam, wanda ke kan hanyar zuwa kudu maso yammacin babban birnin kasar.