Daruruwan jama'a sunyi zanga zanga a Masar

Hakkin mallakar hoto getty images

Daruruwan 'yan uwan wadanda aka kashe ko aka raunata a zanga zangar kasar Misra da ta kai ga hambarradda shugaba Hosni Mubarak sun kara da 'yan sanda a wajen wata kotun da ake yiwa tshohon minsitan cikin gidan kasar shara'a.

Sunyi ta jifan motocin 'yansanda da duwatsu bayan jin cewa an dage shara'ar da ake yiwa tsoshon ministan Habib A' Adli zuwa wata mai zuwa.

Ana dai zargin Habib Al adli ne da baiwa jami'an tsaro umarmin kashe masu zanga zanga.