Masu dauke da ciwon Suga a Najeriya sun yawaita

Wani bincike da aka gudanar a kan ciwon suga a fadin duniya ya gano cewa daga shekarar 1980 zuwa yanzu yawan mutanen da ke dauke da cutar ya ninka fiye da sau biyu, inda ya kai kusan miliyan dari uku da hamsin.

Haka zalika, kimanin mutane miliyan uku ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon kamuwa da ciwon suga a fadin duniya.

Binciken da aka gudanar tare da tallafi daga hukumar lafiya ta duniya W.H.O da kuma gidauniyar Gates Foundation ya gano cewa ciwon suga na ci gaba da karuwa a duniya, lamarin da ka iya kawo cikas ga kudaden da kasashen duniya ke warewa a kasafin kudi domin kula da harkar kiwon lafiya.

A Najeriya kimanin kashi biyar zuwa bakwai cikin dari na al'ummar kasar na fama da ciwon suga, wato kwatankwacin kimanin mutane miliyan bakwai.

Daga cikin abubuwan da Masana suka bayyana dake haddasa ciwon suga, baya ga wadanda ke gadarsa, sun hada da cin abinci barkatai da kuma rashin motsa jiki.

Masana kan cutar dai sun bayyana cewa ciwon suga na haddasa makanta, ko ciwon koda, ko na zuciya, ko kuma ma ciwon kafa.

Kuma Masana sun bayyana cewa ciwon suga na iya kama yara da manya.

Wasu daga cikin alamomin ciwon kamar yanda Masana suka bayyana sun hada da yawan fitsari, ko yawan jin kishirwa ko kuma yawan kuraje a jiki ko rama.