Wen Jiabao na ziyara a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Firayim Ministan China, Wen Jiabao

Firayim Ministan kasar Sin, Wen Jiabao yana wata ziyara a Burtaniya, inda zai tattauna da takwaransa na kasar, wato David Cameron, da kuma manyan jami'an gwamnatin kasar.

Akasarin ziyarar tasa za ta maida hankali ne kan cinikayya tsakanin kasashen biyu.

A yau Lahadi ake sa ran Mista Wen zai kai ziyara mahaifar shahararren mai rubutun adabin nan na Ingila, William Shakespeare, da kuma kamfanin harhada motoci na MG wanda mallakin wani kamfani na kasar China ne.

Sai dai batun siyasa zai taso a cikin ziyarar ne ranar Litinin, yayin da zai ziyarci Firayim Ministan Burtaniya a fadarsa da ke Downing Street.

Kuma da alama babu makawa sai batun kare hakkin bil adama ya taso a cikin tattaunawar da za su yi.

Masana na ganin sakin da gwamnatin kasar Sin ta yiwa wani dan adawa, Hu Jia, na da nasaba da ziyarar da Wen Jibao ke gudanarwa