'Yan bindiga sun kashe mutane 25 a Maiduguri

Muhammad Yusuf
Image caption An kashe shugaban Boko Haram Muhammad Yusuf a shekara ta 2009

Mahukunta sun ce wani hari da aka kai a garin Maiduguri a Arewa maso Gabashin Najeriya, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 25 tare da jikkata wasu da dama.

Sun ce suna kyautata zaton cewa kungiyar Boko Haram ce ta kai harin, wanda ya afku a wata mashaya.

Kungiyar dai na bukatar ganin an kafa cikakken tsarin shari'ar Musulunci a wasu sassan Najeriya.

Ta dauki nauyin hare-hare da dama a Arewacin kasar, ciki harda wanda aka kai a hedkwatar 'yan sanda a Abuja a farkon watan nan.

Wasu mutane biyu a kan babura ne suka kai hari kan wata mashaya da ke cike makil da mutane a ranar Lahadi da dare, a cewar mahukunta.

"Maharan wadanda muke zaton 'yan Boko Haram ne sun wulla bom sannan suka bude wuta kan jama'ar da suka taru a mashayar ta unguwar Dala Kabompi, inda suka kashe mutane 25, yayin da suka jikkata wasu 30," kamar yadda wani dan sanda da ya boye sunansa ya shaida wa AFP.

Wani da ya shaida abinda ya faru Emmanuel Okon ya shaidawa AFP cewa: " Na ji karar fashewar wani abu tare harbe-harben bindiga, yayin da hayaki ya turnuke samaniyar wurin inda jama'a suka fara neman mafaka ko ta ina."

Hari mafi muni da aka taba kaiwa

Har yanzu 'yan sanda ba su bayyana adadin wadanda suka mutu ba.

Amma wakiliyar BBC Bilkisu Babangida ta ce idan har mutane 25 sun mutu, to shi ne hari mafi muni da aka taba kaiwa a garin na Maiduguri.

Ta kara da cewa jama'a na cikin fargaba a garin, ta yadda wasu ke gwammacewa su zauna a gida saboda kada su fita hari ya ritsa da su.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane da dama yawancinsu jami'an tsaro da 'yan siyasa a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar a bara.

Kungiyar na amfani da babura ne wajen kai hare-haren.

Malaman addinin Musulunci da Kirista duka suna fuskantar hare-hare daga kungiyar.

An dai kashe shugabanta Muhammad Yusuf da daruruwan magoya bayansa a Maiduguri a shekara ta 2009, bayan da kungiyar ta kai hari kan jami'an 'yan sanda.