Fandararrun Syria na duba makomar kasar

Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikin na Syria ya haifar da 'yan gudun hijira da dama

Fandararru a Syria sun soma yin taro aDamascus babban birnin kasar, domin tattaunawa a kan yadda kasar za ta koma tafarkin demokradiyya a cikin tsanaki.

Editan gidan talabijin din Barada na 'yan adawan Syrianm ya ce, a kasari taro ne da ya hada kimanin mutane dari, kuma a cikinsu akwai malaman jami'a da 'yan jarida.

Wannan ne taro irinsa na farko a Syrian, tun bayan barkewar zanga-zangar nuna kyamar gwamnati a watan Maris.

Dayawa daga cikin mahalarta taron sun yi zaman kurkuku, saboda irin aikace-aikacensu na siyasa.

Sai dai a wannan karon ba a barazanar kama su saboda ganawar da suke.

Amma su ba wakilai ne na jam'iyyun siyasa ba, kuma ba sa ikirarin wakiltar masu fafutukar da suka bazama kan tituna, suna neman shugaba Bashar Al-Assad ya yi murabus.