Yau ake sa ran fara taron Kungiyar tarayyar Afirka

A yau ne ake sa ran Kungiyar hadin kan Nahiyar Afirka AU za ta gudanar da wani taro a Malabo, babban birnin Equatorial Guinea.

Taron wanda ake sa ran zai sami halartar Shugabannin Kasashen Afirka, zai mayar da hankali ne kan batun samar da ayyukan yi ga matasa a nahiyar.

Matasa a kasashe da dama a nahiyar dai sun nuna cewa zasu iya zama bababr barazana ga shugabanninsu, wadanda suke gani na yin fatali da bukatunsu.

Matasan dai na fatan bayan kammala wannan taro, akalla shugabannin nasu zasu saurari kokensu.

Wasu masana kuma na ganin watakila taron ya karkata ajandar sa zuwa batun Libya, kasar da a halin yanzu ke cikin rikici.

Duk da irin kaurin sunan da Kanar Mu'ammar Gaddafi ya yi wajen halartar tarukan Kungiyar tarayyar Afirka, a wannan karon Shugaban na Libya, wanda ke fuskantar adawar da ke samun goyon bayan Kungiyar tsaron kasashen yammaci ta NATO, ba zai halarci taron na kwanaki biyu da Shugabannin Nahiyar Afirka za su yi ba.

Shugaban hukumar tarayyar Afirka Jean Ping ya ce har yanzu taswirar da kungiyar AU ta tsara a watan Maris din da ya gabata shine mafi a'ala.

Matakin kungiyar AU din dai na kira ne kan tsagaita wuta domin bari a tattauna a siyasance, wadda ta haka ne ka iya kaiwa ga mika mulki.

Sai dai kuma akwai rarrabuwar kawunan dake tsakanin Shugabannin Nahiyar game da matakin ko shin Kanar Gaddafi ya cancanci ya sauka ko kuma ya ci gaba da kasancewa akan mulki, wannan wani batu ne da shima za'a duba.

Sai dai Mr. Ping bai bada wata cikakkiyar amsa ba dangane da tambayar da aka yi masa ta ko shin Kanar Gaddafi zai taka rawa a mika mulkin ba.

Ya dai ce bai kamata 'yan tawayen su saka wadansu sharudda kafin a fara tattaunawa ba, maimakon haka, ya yi kira gare su da su shigo cikin tattaunawar domin a fahimci abin da suke so.

Mr. Ping ya kara da cewa sammacin kama Kanar Gaddafi da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta bayar za ta kara tabarbara lamarin, don haka ne kamar yanda ya bayyana, an yi amfani da kotun ICC din ne wajen bankawa wuta makamashi.

Da yake mayar da martani game da bayar da makamai da Faransa ta yi ga 'yan tawayen Libya, Mr Ping ya ce matakin Faransa abu ne mai hadari, wanda kuma ka iya jefa harkar tsaron yankin a cikin kasada, inda ya yi misali da cewa wannan matakin kamar mayar da Libya Somalia ne.

Wadansu masu nazari dai sun bayyana matakin da saba dokokin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya saka haramcin shigar da makamai Libya.