Tsawa ta halaka mutane da jikkata wasu a Gombe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga Jihar Gombe a arewacin Najeriya na cewa tsawa ta halaka akalla mutane takwas tare da jikkata wasu da dama. Lamarin dai ya faru ne a yankin Karamar hukumar Balanga, bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a jiya da yamma. Bayanan da BBC ta samu na nuni da cewa mutanen da tsawar ta rutsa da su manoma ne wadanda ke aiki a gona, bayan da ruwan saman ya tarar da su, sai suka yi kokakarin fakewa a wuri guda. Kungiyar agaji ta Red Cross ta tabbatar wa BBC mutuwar akalla mutane takwas tare da jikkatar wasu da dama.

Karin bayani:

Jami'in kula da ayyukan taimkawa wadanda bala'i ya shafa a Kungiyar agaji ta Red Cross, a Jihar Gombe, U.B. Ahmed, ya ce suna kokarin taimkawa wadanda suka jikkata, wadanda ya ce ba zai iya bayyana adadin su ba. To sai dai kuma wasu majiyoyi daga asibiti, a yankin na Balanga, na cewa an kwantar da mutane akalla goma sha biyu wanda akasarin su mata ne. Wadanda aka kwantar din dai sun samu kananan raunuka ne, wasu kuma ana lura da su sabo da tsanannin firgita sakamakon bala'in tsawar. Galibin manoma a Najeriya mussamma a yankunan karkara dai kan je gonaki ne su yi aiki da hannunsu, a sabo da rashin na'urorin noma na zamani, kuma wasu kan yi hakan ne a kungiyance. Bala'in na aradu da ya auka wa kananan manoman dai, ba a saba fuskantar irin sa ba a Najeriya, a irin wannan yanayi da ya kai ga hasarar rayuka da jikkatar mutane da dama.