An fara yajin aikin gama-gari a Girka

Girka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yajin aikin ya ritsa da daruruwan 'yan yawon shakatawa

Kungiyoyin kwadagon kasar Girka sun fara yajin aikin gama-gari na kwanaki biyu, kafin kuriar da 'yan Majalisar kasar za su kada kan matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

Fara yajin aikin na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da Fira Minista George Papandreou, ya nemi Majalisar Dokokin kasar da ta amince da sabbin tsauraran matakan tsuke bakin aljihun.

Kungiyoyin bada lamuni na duniya sun ce wajibi ne kasar ta dauki matakan idan har tana son su tallafa mata.

Filayen jiragen sama za su kasance a rufe, sannan jiragen ruwa da jiragen kasa da motocin safa na haya, ba za su yi aiki ba.

Dubun dubatan mutane ne ake sa ran za su kasance a Athens babban birnin kasar.

Wakilin BBC ya ce yayin da Majalisar dokokin kasar ta fara gudanar da muhawara game da tsuke bakin aljihun gwamnati.

Fira Ministan kasar George Papandreou ya yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta samu nasara ba, to hakan na nufin cewa baitul malin kasar zai kare cikin 'yan kwanaki.